Bakonmu a Yau

Dan Majalisar Nijar Murtala Alhaji Mamuda kan kammala aikin Majalisar

Sauti 03:34
Lokacin rantsar da zauren Majalisar a shekarar 2016.
Lokacin rantsar da zauren Majalisar a shekarar 2016. ISSOUF SANOGO / AFP

A Jiya Laraba ne majalisar dokokin kasar Jamhuriyar Nijer ta kawo karshe wa’adin aikinta na tsawon shekaru 5. Majalisar da aka zaba a 2016 zuwa 2021, ta rufe kofofinta ne tare da jawabin da shugabanta Husaini Tinni ya yi  a zauren majalisar dake birnin Yamai. To domin jin Irin muhimman ayuka na gari da za a shaidi majalisar da aikatawa, Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da dan majalisar dokoki Murtala Alhaji Mamuda.