Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Dr Yunusa Muhammad kan cika shekaru 10 da fara rikicin Syria

Sauti 03:27
Wani karamin. yaro mai suna Ahmed dake kukan rasa mahaifinsa Abdulaziz Abu Ahmed Khrer, wanda wani sojan Syria ya kashe.
Wani karamin. yaro mai suna Ahmed dake kukan rasa mahaifinsa Abdulaziz Abu Ahmed Khrer, wanda wani sojan Syria ya kashe. AP - Rodrigo Abd

A yau litinin dubun dubatar mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a garin Idlib da ke matsayin tungar karshe ta ‘yan tawayen kasar Syria, domin tunawa da cika shekaru 10 da barkewar bore, wanda ya rikide zuwa yakin basasa. Alkaluma dai na nuni da cewa akalla mutane dubu 388 ne suka rasa rayukansu a wannan rikici. Dangane da wannan rikici ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Yunusa Muhammad Haruna malami a jami’ar jihar Katsina, kuma masani a game da kasashen Gabas ta Tsakiya.