Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Dr Hakeem Baba-Ahmed kan matsalolin tsaro a Najeriya

Sauti 03:49
Wasu Sojin Najeriya masu yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso gabashin kasar.
Wasu Sojin Najeriya masu yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso gabashin kasar. AFP/File

Yayinda matsalolin rashin tsaro ke neman durkusarda harkokin yau da kullum a fadin Nigeria, bisa dukkan alamu lamarin ya kaima  Gwamnatin Kasar wuya ayanzu, kuma ta sanar da Shirin tunkarar matsalar ayita ta kare. Ministan Tsaro Janar Bashir Magashi ya bada wannan tabbacia wani taro na musamman a Abuja da ya shafi harkan tsaron kasar. Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga bakin Dr Hakeem Baba-Ahmed kakakin Dattawan Arewa ko yaya su ke kallon wannan.