Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Muhammad Hashim Suleiman kan shirin kara kudin man fetur

Sauti 03:15
Wani gidan Man NNPC a Najeriya.
Wani gidan Man NNPC a Najeriya. REUTERS/Stringer

Shugaban Kamfanin mai na Najeriya NNPC Mele Kyari ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da biyan naira biliyan 100 zuwa 120 kowanne wata wajen biyan tallafin man fetur da ake yiwa jama’ar kasar ba. Jami’in ya ce yin haka zai sanya farashin man ya kai naira 234 kowacce lita, matakin da tuni ya harzuka wasu jama’ar kasar. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da malam Muhammad Hashim Suleiman na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.