Bakonmu a Yau

Jami’an 'Yan Sanda 497 aka kashe lokacin da suke gudanar da ayyukan a Najeriya

Sauti 03:40
Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde tare jami'an 'Yan Sandan Najeriya
Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde tare jami'an 'Yan Sandan Najeriya Twitter@seyiamakinde

Wani rahotan bincike da aka gudanar a Najeriya ya bayyana cewar jami’an Yan Sanda 497 aka kashe lokacin da suke gudanar da ayyukan su a cikin shekaru 6 da suka gabata.

Talla

Rahotan da kungiyar SBMorgan dake sanya ido kan harkokin tsaro ta wallafa yace an kuma kashe akalla fararen hula 1,175 a hare haren da aka gani a sassan kasar daga ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2015 zuwa 22 ga watan Maris na wannan shekarar.

Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba

Dangane da wannan batu Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Tsohon Sufeto Janar na Yan Sandan kasar Alhaji Suleiman Abba, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.