Tattaunawa da Mahamoudou Djibo kan rantsar da sabon shugaban Nijar

Sauti 04:24
Sabon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.
Sabon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum. AFP - ISSOUF SANOGO

Yau juma’a aka rantsar da Mohamed Bazoum a matsayin shugaban kasa na 10 a Jamhuriyar Nijar, bikin da ke matsayin karo na farko da wani zababben shugaba ke mika mulki ga wani shugaba da aka zaba a kan tafarkin dimokuradiyya a kasar.To sai dai ko shakka babu shugaba Bazoum ya karbi ragamar mulkin ne a wani yanayi da ‘yan adawa ke ci gaba da nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da ya gabata.To a game da haka ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da PHD Mahmoudou Djibo, malami a jami’ar Yamai, ga kuma zantawarsu.