Tattaunawa da CP Muhammad Indabawa kan matsalolin tsaron Najeriya

Sauti 03:22
Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos

Gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan awaren kungiyar IPOB masu neman kafa kasar Biafra, sun kai hare-hare kan babban gidan yarin Imo inda suka saki fursunoni mau yawa.

Talla

‘Yan bindigar haye cikin akalla motoci 10 sun kuma  kone sassan Hedikawatar ‘yan sandan jihar Imo, tare da kuma kai hari kan shingen sojojin dake babbar hanyar da ta sada birnin Owerri da Onitsha.

Nura Ado Suleiman ya tattauna da Muhd Indabawa, tsohon kwamishinan ‘yan sanda a Najeriya kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke karuwa a yankin kudu maso gabashin Najeriya, a yayin da ake fama da matsalolin tsaron arewacin Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.