Tattaunawa da Pastor Yohanna Buru kan bukukuwan Easter a sassan Duniya

Sauti 03:17
Fafaroma Francis yayin bikin Easter a fadarsa.
Fafaroma Francis yayin bikin Easter a fadarsa. via REUTERS - VATICAN MEDIA

Yau Kiristocin Duniya ke kammala bukukuwan Easter, kuma shugaban Mabiya darikar Katlika na Duniya Fafaroma Francis ya bukaci mabiyan sa da su cigaba da jajircewa, yayin da ya ke bayyana maganin rigakafin cutar corona a matsayin babban makamin yaki da cutar.

Talla

Yayin da ya ke gabatar da jawabin sa kan bikin Easter, Fafaroman da ke jagoranci mabiya darikar ta Katlika sama da biliyan guda da miliyan 300 a Duniya ya bukaci ganin an samarwa kasashe matalauta maganin da kuma kawo karshen yake-yaken da ake samu a wasu kasashen Duniya ciki har da tashin hankalin Najeriya.

Dangane da muhimmancin wannan biki, mun tattauna da Pastor Yohanna Buru, daya daga cikin shugabannin kiristocin Najeriya kuma ga tsokacin da ya yi akai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.