Bakonmu a Yau

Haramtattun makamai fiye da miliyan 6 sun bazu a Najeriya- Abdulsalami

Sauti 03:59
Abdusalami Abubakar ya ce fatar su ita ce Najeriya ta samo hanyar shawo kan wadannan matsaloli ta hanyar tintiba da kuma sauraron shawarwari wadanda za su taimaka wajen karfafawa jama’a gwuiwa.
Abdusalami Abubakar ya ce fatar su ita ce Najeriya ta samo hanyar shawo kan wadannan matsaloli ta hanyar tintiba da kuma sauraron shawarwari wadanda za su taimaka wajen karfafawa jama’a gwuiwa. AFP PHOTO/ TONY KARUMBA

Tsohon shugaban Najeriya Abdulsalami Abubakar ya yi shelar cewar yanzu haka akwai haramtattun makaman da ke hannun jama’ar da bai dace ace sun mallake su ba da suka kai miliyan 6 a sassan kasar.

Talla

Yayin da ya ke tsokaci wajen taron masu ruwa da tsaki kan zaman lafiyar Najeriya, tsohon shugaban ya ce karuwar makamai sun dada zafafa matsalolin tsaron da suka addabi kasar wadanda suka yi sanadiyyar hallaka rayukan mutane sama da dubu 80.

Abdulsalami Abubakar ya ce matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya a yanzu su na da yawa sosai da suka hada da rikicin boko haram da 'yan bindiga barayin shanu da masu garkuwa da mutane da talauci da masu bukatar raba kasa ga kuma yunwa sakamakon hana manoma zuwa gonakin su abinda ya jefa mutane cikin kakanikayi.

Dangane wadannan kalamai na tsohon shugaban Najeriyar Abdulsalami Abubakar ne Wakilinmu Muhammad Sani Abubakar ya zanta da shi ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.