Kafa rundunonin tsare yankunan Najeriya ba cigaba bane - Dakta Hakeem

Sauti 03:22
Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya. © @Hope_Uzodimma1/Premium Times

A kokarinsu na kawo karshen matsalar tsaron da ke karuwa a yankin su, Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya a karkashin jagorancin gwamnan Ebonyi Dave Umahi a jihar Imo, sun sanar da kafa rundunar tsaron da suka sanyawa suna EBUBE AGU wadda suka dorawa alhakin murkushe barazanar jama’ar yankin ke fuskanta daga masu aikata muggan laifuka.

Talla

Matakin gwamnonin ya haifar da muhawara, inda wasu ke yabawa da matakin bisa cewar sun yi daidai, a yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin alamar dake kara nuna gazawa daga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Yayin tsokaci kan halin da ake ciki a lokacin tattaunawa da Garba Aliyu Zaria, Dakta Hakeem Baba-Ahmed kakakin kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ya bayyana kafuwar sabbin rundunonin tsaron yankuna cigaban mai hakon rijiya ne, domin kamata yayi gwamnati ta sauke nauyin da yake kanta na inganta tsaro ta hanyar kara yawan jami’an tsaron da kuma basu kayan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.