Tattaunawa da Hosaya Sambido kan fafutukar kubutar da 'yan matan Chibok

Sauti 03:39
Wasu daga cikin 'yan Matan Sakandiren Chibok da Boko Haram ke ci gaba da tsarewa.
Wasu daga cikin 'yan Matan Sakandiren Chibok da Boko Haram ke ci gaba da tsarewa. Reuters/Akintunde Akinleye

Kungiyar Iyaye, da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace a makarantar Sakandaren Chibok a jihar Borno, shekaru bakwai da suka gabata sun lashi takobin ci gaba da fafutukan ganin an kubutar da ‘yan matan da suka rage hannun mayakan kungiyar ta Boko Haram.Dangane da wannan Garba Aliyu Zaria ya tattauna da shugaban Kungiyar da ke fafutukar ganin an kubutar da 'yan matan fiye da 250 Hosaya Sambido ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.