Matsayin ECOWAS kan zaben shugabancin Jamhuriyar Benin

Sauti 04:30
Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon yayin jefa kuri'asa a zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar 11 ga watan Afrilun 2021.
Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon yayin jefa kuri'asa a zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar 11 ga watan Afrilun 2021. REUTERS - STRINGER

Tawagar ‘yan kallo da kungiyar kasashen Yammacin Afirka Ecowas ta tura don sa-ido a zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar lahadin da ta gabata a jamhuriyar Benin, ta bayyana matsayinta a game da zaben, wanda aka yi cikin yanayi na tankiya tsakanin bangaren gwamnati da kuma na ‘yan adawa.Honorable Boukary Sani Zilly, mataimakin shugaban majalisar dokokin Ecowas, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal matsayin tawagarsu dangane da wannan zabe.