Janar Yarima ya musanta rahoton tserewar dubban mutane daga Damasak

Sauti 03:33
Wani yanki dake wajen garin Damasak dake jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wani yanki dake wajen garin Damasak dake jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya. AP - Jerome Delay

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane 65,000 suka fice daga garin Damasak dake Jihar Barnon Najeriya domin tsira da rayukan su bayan hare haren da mayakan boko haram suka kai har sau uku cikin mako guda.

Talla

Babar Balock, kakakin hukumar kula da yan gudun hijira na Majalisar yace hare haren sun tilastawa akalla kashi 80 na mazauna Damasak barin garin.

Dangane da wannan rahoto, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya Janar Muhammad Yarima, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.