Dokta Yakubu Ahmed BK kan matsalar satar dalibai a arewacin Najeriya

Sauti 03:56
Wani hoton abin misalin dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoton abin misalin dake nuna 'yan bindiga. © PHOTO/FOTOSEARCH

Wasu kafofin yada labarai a Nigeria sun sanar da cewa wasu dangi da ‘yan uwan daliban Jami’ar Greenfield  mai zaman kanta dake  Kaduna sun ce ‘yan bindigan da suka sace dalibai 23 kafin wayewar garin Laraba sun bukaci a bas u kudin fansa har Naira miliyan 800 kafin su sako su.Rundunar ‘yan sandan jihar kaduna dai sun gaskata satan daliban, amman kuma ba su yi Karin haske ba.Mun nemi ji daga Yakubu Ahmed BK mai sharhi dangane da harkokin tsaro a Nigeria yadda yake kallon annobar satar dalibai dake dada kamari a arewacin Nigeria.