Tattaunawa da Tijjani Baba Gamawa kan kisan Sojin Najeriya 31 a Mainok

Sauti 03:59
Sojin Najeriya a yakinsu da Boko Haram.
Sojin Najeriya a yakinsu da Boko Haram. © Lekan Oyekanmi/AP

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewar akalla sojoji 31 suka rasa rayukan su sakamakon kazamin harin da mayakan Boko haram ko kuma ISWAP suka kai kan tawagar sojojin Najeriya da ke dauke da makamai zuwa Maiduguri a garin Mainok.

Talla

Bayanai sun ce wadannan mahara sun yi amfani da muggana makamai wajen kai harin wanda ya basu damar kashe sojojin Najeriya da kuma kwashe makamai.

Dangane da wannan hari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.