Dr. Elharun kan taimakon da Najeriya ke nema daga Amurka

Sauti 03:44
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden yayin wata ziyara da Buhari ya kai Amurka lokacin shugaba Barack Obama
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden yayin wata ziyara da Buhari ya kai Amurka lokacin shugaba Barack Obama © Presidency of Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci taimakon Amurka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi nahiyar Afirka baki daya, inda ya roke ta da ta dawo da Cibiyar rundunarta da ke kula da Afirka daga Jamus zuwa nahiyar. A tattaunawar da suka yi da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken Buhari ya ce, dawo da Cibiyar Rundunar Afirka zai taimaka wajen dakile matsalolin tsaron da suka mamaye nahiyar. A game da wannan batu Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. El Harun Muhammed, masanin siyasar duniya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar