Bashir Nuhu Mabai a kan shirin kyakkyawar dangantaka tsakanin Iran da Saudiyya

Sauti 03:37
Yerima Mohammed bin Salman. na Saudiyya.
Yerima Mohammed bin Salman. na Saudiyya. AP - Mandel Ngan

 Saudi Arabia ta bayyana aniyar ta na samun dangantaka mai kyau da babbar abokiyar gabar ta wato kasar Iran kamar yadda Yarima Mohammed ibn Salman ya sanar.Yariman ya ce Saudiya da kawayen ta na duniya na aiki tare wajen shawo kan matsalolin da suka shafi irin halayen da Iran ke nunawa da shirin ta na samun makamin nukiliya da harba makamai masu linzami da taimakawa kungiyoyin ‘yan ta’adda da aka haramta.Dangane da wannan matsayi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Bashir Nuhu Mabai na Jami’ar Dutsinma dake Katsina, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.