Tattaunawa da Mustapha Jokolo kan neman taimakon Amurka ga tsaron Najeriya

Sauti 03:43
Al'amuran tsaro na ci gaba da tabarbarewa a sassan Najeriyar musamman arewaci.
Al'amuran tsaro na ci gaba da tabarbarewa a sassan Najeriyar musamman arewaci. AP - Sunday Alamba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci taimakon Amurka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi nahiyar Afirka baki daya, inda ya roke ta da ta dawo da Cibiyar rundunar ta da ke kula da Afirka daga Jamus zuwa nahiyar.

Talla

A tattaunawar da suka yi da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken Buhari ya ce dawo da Cibiyar rundunar Afirka zai taimaka wajen dakile matsalolin tsaron da suka mamaye nahiyar.

Dangane da wannan bukata, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Mai Martaba Sarki Gwandu na 19 Manjo Almustapha Haruna Jokolo, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.