Dr. Shu'aibu Shinkafi kan halin rashin tsaro da jihar Zamfara ke fuskanta

Sauti 03:39
Dr Suleiman Shuaibu Shinkafi daya daga cikin jiga jigan Yan Jihar Zamfara a Najeriya yayin wata ziyara ofishin RFI hausa, 01 ga watan Mayu 2021
Dr Suleiman Shuaibu Shinkafi daya daga cikin jiga jigan Yan Jihar Zamfara a Najeriya yayin wata ziyara ofishin RFI hausa, 01 ga watan Mayu 2021 © Rfi hausa - Ahmed Abba

Yayin da matsalar tsaro ke cigaba da ta’azzara a sassan Najeriya, musamman Yankin arewacin kasar, ana cigaba da matsin lamba wa gwamnatin tarayya wajen ganin ta kara daukar matakai masu tsauri wajen dakile matsalar domin ceto rayuka.

Talla

A makon jiya kawai akalla mutane 240 'Yan bindiga suka kashe a hare hare daban daban, kuma akasarin su sun fito ne daga Jihar Zamfara inda gwamnati ke ikrarin sasantawa da 'yan bindigar.

A karshen makon da ya gabata, daya daga cikin jiga jigan 'Yan Jihar, Dr Suleiman Shuaibu Shinkafi ya ziyarci ofishin mu, kuma Editanmu Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi, kuma ga tsokacin da ya yi akan matsalar Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI