Buba Galadima kan yadda sojoji suka nisanta kansu da yunkurin juyin mulki

Sauti 03:46
Engr Buba Galadima na Jam'iyyar PDP a Najeriya
Engr Buba Galadima na Jam'iyyar PDP a Najeriya News Dairy

Sojojin Najeriya sun yi watsi da kiran da wasu ke yi na cewa su karbi mulkin kasar saboda abin da suka kira gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari na shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Talla

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar tsaron kasar Janar Onyema Nwachukwu, sojojin sun tabbatar da goyon bayansu ga gwamnatin dumokuradiyya mai-ci, inda suke cewa babu wani tunani na hambarar da gwamnatin farar hula. Dangane da halin da ake ciki ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Injiniya Buba Galadima, jigo a Jam’iyyar PDP mai adawa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.