Fassarar tattaunawar Mr Nnamdi Obasi na ICG kan rikicin makiyaya da manoma

Sauti 03:35
Wasu Fulani makiyaya a Najeriya.
Wasu Fulani makiyaya a Najeriya. REUTERS/Akintunde Akinleye

Kungiyar ICG da ke sanya ido kan rikice rikice ta bayyana damuwa dangane da rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya ganin yadda matsalar ke kaiga rasa rayuka sakamon sauyin yanayi da karuwar jama’a da rikicin boko haram da kuma hare haren Yan bindiga da suka tilastawa makiyaya barin yankin arewacin kasar zuwa kudu, abinda ya hada su rikici da manoman.

Talla

A shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin shekaru 10 na bunkasa harkar kula da kiwo domin hana makiyaya tafiye tafiye da inganta kiwo da kuma kawo karshen rikice rikicen, amma wasu matsaloli sun hana shirin tasiri.

Dangane da rahotan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da  Mr Nnamdi Obasi, jami’i ne a kungiyar ta ICG, kuma ga tsokacin da yayi akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI