Tattaunawa da Dr Yahuza Ahmad Getso kan yawaitar masu tada kayar baya a Najeriya

Sauti 04:04
Matsalolin tsaro na ci gaba da tsananta a kusan ilahirin sassan Najeriya.
Matsalolin tsaro na ci gaba da tsananta a kusan ilahirin sassan Najeriya. © Social News XYZ

A yayin da Gwamnatin Najeriya ke kokarin shawo kan matsalar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashi da yammacin kasar, sai ga ‘yan aware masu neman kafa kasar Biafra daga kasar sun zafafa tayar da kayar baya, inda a cikin watanni 4 rahotanni ke nuna yadda suka kashe 'yan sanda sama da 120 baya ga tsananta hare hare. Kan hakan ne Michael Kuduson ya tattauna da Dr Yahuza Ahmad Getso, mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriyar.