Ɗangote ya ƙaddamar da shirin horas da matasan Najeriya sana'o'i

Sauti 02:31
Ahmed Abba na RFI tare da Hamshakin attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote, 5 ga watan Maris 2021
Ahmed Abba na RFI tare da Hamshakin attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote, 5 ga watan Maris 2021 © Rfi hausa - Ahmed Abba

Gidauniyar attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote, ta kaddamar da wani shirin hadin guiwa da wata takwararta dake kasar Jamus VDMA, don horas ta matasan Najeriya ayyukan hannu, kamar su gyaran na’urorin lantarki da injuna.

Talla

Ana saran shirin ya rage dogaro da akayi da kasashen waje wajen samun kwarrun injiniyoyin gyaran injunan kamfanoni da masana’antun a cikin gida.

Gidauniyar attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote, ta kaddamar da wani shirin hadin guiwa da wata takwararta dake kasar Jamus VDMA, don horas ta matasan Najeriya ayyukan hannu, kamar su gyaran na’urorin lantarki da injuna, ranar 02 ga watan Yuni 2021
Gidauniyar attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote, ta kaddamar da wani shirin hadin guiwa da wata takwararta dake kasar Jamus VDMA, don horas ta matasan Najeriya ayyukan hannu, kamar su gyaran na’urorin lantarki da injuna, ranar 02 ga watan Yuni 2021 © Rfi hausa - Ahmed Abba

A cewar Hamsashikin attajirin na Afrika Alhajii Aliko Dangote, Shirin zai lakume kimanin EURO miliyan 7, wajen daukar nauyin matasan da aka zakulo a shiyoyin Najeriya 6, kuma kason farko ya kunshi ‘matasa 120.

Hamshakin attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote, 02 ga watan Yuni 2021
Hamshakin attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote, 02 ga watan Yuni 2021 © Rfi hausa - Ahmed Abba
Bukin kaddamarwar da ya gudana a kasaitattacen Otel EKO dake birnin Lagas, ya samu halartan manyan baki daga ciki da wajen Najeriya, ciki harda shugaban kungiyar injiniyoyin masu kere-kere da masa’antun kasar Jamaus VDMA, Dr. Reinhold Festge, wanda ya tabbatar mini cewar Shirin zai kasance na dogon zango.

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikekken hirar da muka yi da Dangote a tattaunawarsa da Ahmed Abba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI