Dr. Abbati Bako kan tsawaita wa'adin Guterres
Wallafawa ranar:
Sauti 03:46
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince ba tare da hamayya ba domin bai wa Sakatare Janar Antonio Guterres damar yin wa’adi na biyu domin ci gaba da tunkarar matsalolin da suka addabi duniya musamman rikice-rikicen da ake fama da su. Guterres wanda tsohon Firaministan Portugal ne ya karbi aikin jagorancin majalisar ne a shekarar 2017 daga hannun Ban Ki Moon, Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Dr. Abbati Bako mai sharhi kan siyasar duniya