Tattaunawa da Sharzali Sunusi Suleiman kan harajin kamfanonin sada zumunta

Sauti 04:01
Matakin fara shirin karbar haraji daga kamfanonin sada zumuntar ya biyo bayan dambarwar da ta kunno kai tsakanin Twitter da gwamnatin Najeriya.
Matakin fara shirin karbar haraji daga kamfanonin sada zumuntar ya biyo bayan dambarwar da ta kunno kai tsakanin Twitter da gwamnatin Najeriya. Lionel BONAVENTURE AFP/File

Gwamnatin Tarayyar Najeria ta ce daga yanzu dole ne dukkannin kafofin sada zumunta a kasar, kamar su Twitter da Facebook da sauransu, su yi rajista, a wani mataki na sa ido a kan abubuwan da ke gudana a cikinsu.

Talla

Michael Kuduson ya tattauna da masanin harkar sadarwar zamani daga cibiyar bunkasar kimiyyar sadarwar zamani ta CITAD a Najeriya, Sharzali Sunusi Suleiman ya shaida wa Michael Kuduson cewa gazawar gwamnati wajen kai korafi a duk lokacin da aka karya dokar kasa a dandalin sada zumunta ne ya sa aka kai wannan matsayi na rashin jituwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.