Alkasim Abdurrahman: Kan janye sojojin Faransa daga Sahel

Sauti 03:51
Sojojin Faransa masu yaki da ta'addanci a Sahel
Sojojin Faransa masu yaki da ta'addanci a Sahel AP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana shirin janye dakarun kasarsa da ke yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel na kusan shekaru 10 a karkashin rundunar Barkhane. Amma Macron din ya ce,  za a  kafa wata sabuwar runduna ta sojojin kasashen duniya mai suna Takuba wadda za ta kunshi daruruwan sojojin kasar. Kuna iya latsa alamar sautin domin sauraren cikakkiyar hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da masanin harkar tsaro Alkasim Abdurrahman daga Jamhuriyar Nijar.