NNPC: Injiniya Kailani game da zargin almundahana a harkar mai

Sauti 03:34
Wani sashe na matatar mai (NNPC) a Najeriya
Wani sashe na matatar mai (NNPC) a Najeriya Africanews

Wasu ‘yan Najeriya sun kaddamar da kamfen neman ganin an samu sauyi a shugabancin kamfanin man NNPC mallakin gwamnatin kasar saboda zarge-zargen da suke kan yadda ake tafiyar da shi. Sai dai wasu masu ruwa da tsaki a harkar man da iskar gas na danganta zargin da siyasa da kuma neman ganin an yi wa shugabancin zagon kasa sakamakon tsarin da ya dauko na inganta aikinsa. Danna alamar sauti don sauraren tattaunar Engr. Kailani Muhammad kwararre game da harkar mai a Najeriya da Bashir Ibrahim Idris.