Bakonmu a Yau

Dr. Isa Abdullahi kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Sauti 03:40
Kayayyakin masarufi
Kayayyakin masarufi © Pixabay/CC

Bankin Duniya yace hauhawan farashin kayan masarufi a Najeriya yayi sanadiyar jefa jama’ar kasar miliyan 7 zuwa tsananin talauci. Rahotan bankin wanda ya yabawa hukumomin Najeriya saboda matakan da suka dauka na rage radadin matsalar da annobar korona ta haifar, ya kuma bukaci hukumomin da suka kara kaimi wajen dakile tsadar kayayyakin da mutane ke bukata na yau da kullum.

Talla

Rahotan Bankin da yayi amfani da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Bada Lamuni ta duniya yace kashi 41 na Yan Najeriya ko kuma mutane miliyan 87 na fama da tsananin talauci wajen rayuwa a kasa da Dala 2 kowacce rana.

Danna alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Dr. Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki a Jami’ar Kashere ta Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.