Bakonmu a Yau

Miyatti Allah ta yi tir da harin sojoji da ya hallaka shanu dubu a Nasarawa

Sauti 04:03
Makiyaya a Jamhuriyyar Nijar yankin Sahara
Makiyaya a Jamhuriyyar Nijar yankin Sahara Getty Images/The Image Bank/Philippe Bourseiller

A Najeriya, jiragen saman yakin soji biyu sun yi luguden wuta a kan wasu matsugunan Fulani a kananan hukumomin keana da Doma na jihar Nasarawa, har ma ake zargin sama da shanu 1000 sun salwanta, kana wasu makiyaya suka dan ji jiki. A kan haka ne Michael kuduson ya tuntubi mukaddashin shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Nasarawa, Alhaji bala muhammed Dabo, kuma kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikekken hirar da mukayi da shi.