Bakonmu a Yau

Majalisar Wakilai ta tantace sabon hafsan sojin kasa na Najeriya

Sauti 03:17
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya. AUDU MARTE / AFP

Majalisar Wakilan Najeriya ta tantance sabon babban hafsan sojin kasa Janar Faruq Yahaya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada domin maye gurbin Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu. Dangane da kalubalen dake gaban sabon shugaban sojin da kuma tabarbarewar matsalar tsaro a kasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon. Abdurazaq Namdas, shugaban kwamitin sojin kasa, na Majalisar, kuma kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron hirar da akayi da shi.