Shugabannin Turai na kokarin gyara alakarsu da Rasha

Sauti 03:41
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. AFP - STEPHANIE LECOCQ

Kasashen Jamus da Faransa na kokarin shawo kan shugabannin kungiyar Tarayyar Turai don ganin sun sake bude wani sabon babin gyara alakarsu da Rasha, wajen shirya ganawa da Shugaba Vladimir Putin.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da kansa ke cewa zaman lafiyar yankin ya ta’allaka ne wajen tattaunawa da Rasha, yayin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta shaidawa majalisar dokokin kasar muhimmacin tattaunawa da Rasha.

Tuni gwamnatin Kremlin tayi maraba da wannan tayi na tattaunawa.

Dangane da wannan bukata na Turai, Ahmad Abba ya tattaunawa da Farfesa Kamilu Sani Fage masanin siyasar Duniya a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.