Bakonmu a Yau

Usman Muhammad kan ganawar Ouattara da Gbagbo a Abidjan

Sauti 03:35
Shugaban Ivory Coast Alassane Outarra da Laurent Gbagbo.
Shugaban Ivory Coast Alassane Outarra da Laurent Gbagbo. AFP - ISSOUF SANOGO,SIA KAMBOU

A Ivory Coast, jagororin al’umma 2 da  suka dade ba sa ga-maciji da juna, shugaban kasar mai ci, Alassane Ouattara da tsohon shugaba Lauren Gbagbo sun gana a Abdijan a karon farko tun bayan da kasar da ke yammacin Afrika ta fada mummunar rikicin siyasa da ya lakume  rayuka sama da dubu 3.Kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da masanin siyasar kasa da kasa, Dr. Usman Muhammad, na cibiyar nazarin dimokaradiyya da ke Abuja.