Da Rabon Ganawa
Manufar shirin Da Rabon Ganawa ita ce sake sada mutanen da suka rabu da iyalansu a sakamakon tashe-tashen hankula a yankin Tafkin Chadi musamman a arewa maso gabashin Najeriya. Kungiyar Agaji ta ICRC da RFI sun yi hadin guiwa domin sake sada wadannan mutane da 'yan uwansu. Za a rika watsa shirin da misalin karfe 7 da minti 20 na safiyar ranar Alhamis, sannan a maimaita a ranar Juma'a da misalin karfe 8 da minti 20 na safe. Kuna iya ziyartar shafin ICRC www.icrc.org/nigeria.
Dukkanin shirye-shirye