Kasuwanci

Sabuwar Kasuwar Akinyele ta kankama a Ibadan bayan watsewar Sasa

Sauti 09:58
Sabuwar Kasuwar Akinyele dake Ibadan na jihar Oyo a Kudu maso yammacin Najeriya, inda hausawa suka koma bayan rikicin su da yarbawa a Sasa
Sabuwar Kasuwar Akinyele dake Ibadan na jihar Oyo a Kudu maso yammacin Najeriya, inda hausawa suka koma bayan rikicin su da yarbawa a Sasa © Rfi hausa / Ahmed Abba

Shirin Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba, ya yada zango ne garin Ibadan na jihar Oyo dake kudu maso Yammacin Najeriya, inda ya leka sabuwar kasuwar Akinyele, inda wasu hausawa suka koma bayan hatsaniyar da aka samu a kasuwar SASA da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi.

Talla

Duk da cewar, Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya bude Kasuwar Sasa a hukumance, bayan da aka rufeta sakamakon hatsaniyar da aka samu, babu alamar cewar wadanda ke Akinyele yanzu haka, na da niyyar komawa su hade da takwarorinsu na Sasa, bayan wannan rikici da ake dangantashi da Kabilanci ko neman shugabanci, domin suna cewa sabuwar kasuwar gaba ta kai su..

Sabuwar Kasuwar Akinyele dake Ibadan na jihar Oyo, inda Hausa suka koma bayan kaura daga Sasa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.