Yadda Boko Haram ta hana al'ummar Barno samun wutan lantarki

Sauti 10:03
Manyan layukan wutan lantarki a Najeriya
Manyan layukan wutan lantarki a Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' tare da Ahmed Abba ya yada zango ne jihar Barno dake Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ya yi nazari kan halin da al’umma suka shiga masamman a wannan lokaci na watan Ramadana, sakamkon rashin wutan lantarki da suka kwashe sama da watanni uku suke ciki, bayan da Boko Haram ta lalata turakun da ke kai wutan lantarki jihar.