Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Lafiya Jari ce Duniya na ganin karuwar masu fama da cutar karkarwar jiki ta Parkinson Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar karkarwar jiki ko kuma Parkinson a turance wadda wasu ke alakantawa da yawan shekaru, inda a yanzu haka ake da jumullar mutane fiye da miliyan 10 da ke fama da ita.22/05/2023 10:13
-
Lafiya Jari ce Cutar TB ko tarin fuka na ci gaba da yaduwa a sassan Najeriya Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan karuwar masu fama da cutar tarin fuka ko kuma TB da ke ganin bazuwarsa a sassan Najeriya duk kuwa da gangamin yaki da cutar da gwamnatoci ke yi.15/05/2023 10:00
-
Lafiya Jari ce Yadda karancin takardun Naira ya shafi mara lafiya a asibitocin Najeriya Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba yadda matsalar sauya wasu takardun kudin Nairar Najeriya da tsadar rayuwa suka shafi harkokin asibiti masamman majinyata ko masu bukatar gaggawa a asibiti.10/04/2023 10:08
-
Lafiya Jari ce Shawarwarin masana kan nau'ikan cutukan da ke barazana a lokacin Azumi Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutukan da ke tasiri a lokacin azumun watan Ramadan dama nau'ikan abincin da ya kamata masu irin cutukan su rika ma'amala da su.03/04/2023 10:25
-
Lafiya Jari ce Ana fuskantar karancin jinin tallafi a asibitocin jamhuriyyar Nijar Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda wasu asibotoci a Jamhuriyyar Nijar ke fama da karancin jini sakamakon rashin masu bayar da gudunmawar jinin don tallafawa marasa lafiya.27/03/2023 10:18
-
Lafiya Jari ce Ta'ammuli da miyagun kwayoyi na kara yawan masu tabin hankali a Nijar Shirin "Lafiya jari ce" na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsalar shaye-shaye sannu a hankali ke ci gaba da jefa tarin matasa a lalurar hauka ko kuma tabin hankali, matsalar da ke ci gaba da tsananta a sassan Jamhuriyya Nijar musamman tsakanin matasa ko kuma daliban jami’o’i. Alkaluman ma’aikatar lafiyar Nijar na nuna yadda ake da tarin matasa da yanzu haka ke karbar maganin cutar kwakwalwa galibinsu sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi ko kuma shaye-shayen zamani.13/03/2023 10:18
-
Lafiya Jari ce Yadda jama'a za su bai wa lafiyarsu kariya a lokacin zabe Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wanna mako ya kawo mana yadda jama'a za su duba lafiyarsu ne a lakcin zabuka. Wannnan maudu'i na zuwa ne bisa la'akari da yadda jama'a da dama suka samu rauni, wasu kuma suka mutu saboda tarzomar da ta tashi a lokacin zaben shugaban kasa a Najeriya.06/03/2023 10:07
-
Lafiya Jari ce An samu karuwar cutar Gout a tsakanin 'yan Najeriya Shirin Lafiya Jari Ce na wannan lokaci ya tattauna akan cutar Gout da ke kumbura sassan jikin Dan Adam ciki kuwa har da jjijiyoyi.20/02/2023 10:22
-
Lafiya Jari ce Kalubalen kula da masu cutar farfadiya a kasashe masu tasowa Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar farfadiya ko kuma Epilepsy a turance, cutar da ke matsayin babbar barazanar lafiya ga jama'a musamman a kasashe masu tasowa da ke karancin kulawar lafiya.13/02/2023 10:01
-
Lafiya Jari ce Asibitocin Najeriya za su fara amfani da tsarin neman ganin likita ta wayar Salula Shirin lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba wani ci gaban lafiya da aka samu a Najeriya bayan da hadaka tsakanin ma'aikatar lafiya da hukumar sadarwa ya kai ga samar da wata manhaja wadda za ta saukakawa marasa lafiya samun damar ganin likita tun gabanin su je asibiti, a wani yunkuri na dakile cunkoson da ake samu a asibitocin kasar.06/02/2023 10:00
-
Lafiya Jari ce Yadda jihar Yobe ta samu tagomashin sabbin asibitoci da kayakin kula da lafiya Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan ci gaban lafiyar da aka samu a jihar Yobe a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, bayan da gwamnatin jihar ta samar da sabbin asibitoci da kuma horar da malaman jinya don dakile matsalolin lafiyar da jihar ke fuskanta.30/01/2023 09:51
-
Lafiya Jari ce Najeriya ta fi yawan kutare a Afrika Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari ne kan sake bazuwar cutar kuturta a Najeriya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kasar ce ke kan gaba wajen yawan kutare a kasashen Afrika.23/01/2023 09:54
-
Lafiya Jari ce Yadda mutane ke boye cutar sankarar mama A Najeriya ana ci gaba da samun matsalar cutar sankarar mama, cutar d har yanzu babu takamammen maganinta duk kuwa da cewa daya bisa uku na matan duniya na cikin hadarin kamuwa da ita. Har yanzu dai kwararru sun gaza gano aininhin abin da ke haddasa wannan cuta, sai dai sun ce sun gano dalilan da suka sa take kama wasu nau'ukan mata fiye da wasu.28/11/2022 10:15
-
Lafiya Jari ce Yadda mutane ke boye cutuka masu nasaba da kwakwalwa Shirin 'Lafiya Jari ce' ya mayar da haankali ne a kan yadda mutane ke boye cutukan da ke damunsu har su kai ga ta'azzara a jikinsu, musammam cutukan da suka shafi kwakwalwa. sau da damu a cikin al'ummarmu, mutane ba sa zuwa ganin likitan kwakwalwa, ko kuma kaai 'yaan uwansu, don kawai kada a danganta su da laallurar tabin hankali.31/10/2022 10:41
-
Lafiya Jari ce Kashi 50 na kananan yara a arewacin Najeriya na fama da cutar yunwa ko Tamowa Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda cutar tamowa ko kuma yunwa sakamakon rashin abincin mai gina jiki ke kashe yara miliyoyin kananan yara duk shekara inda a baya-bayan nan wasu alkaluman MSF ke nuna yadda kusan kashi 50 na yaran arewacin Najeriya ke fama da wannan cuta. Ayi saurare Lafiya.24/10/2022 10:57
Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.