Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya mutu yana da shekaru 99

Sauti 19:44
Marigayi Yarima Philip tareda rakiyar sarauniyar Ingila a shekara ta 2011
Marigayi Yarima Philip tareda rakiyar sarauniyar Ingila a shekara ta 2011 © AFP/Stephan Rousseau

A cikin shirin mu zagaya Duniya ,Garba Aliyu Zaria ya mayar da hankali ga fadar Ingila,yan lokuta bayan da sanar da mutuwar Yarima Philip ya na mai shekaru 99 a Duniya.

Talla

Mutuwarsa  na zuwa ne a yayin da ya rage watanni kalilan a gudanar da bikin cikarsa  shekaru 100 da haihuwa a cikin watan Yuni mai zuwa.

Fadar Sarauniyar Ingila
Fadar Sarauniyar Ingila JUSTIN TALLIS AFP

Yariman ya auri Sarauniya Elizabeth a shekarar 1947, wato shekaru biyar kafin ta dare kan gadon sarautar Ingila, yayin da  ma’auratan biyu suka kafa tarihin zama masu mulki mafi dadewa kan karaga a tarihin Birtaniya.

Ma’auratan biyu na da yara hudu da jikoki takwas da kuma tattaba-kunni 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.