Yadda sare itatuwa ke karfafa barazanar kwararowar Hamada a birane

Sauti 20:18
Barazanar kwararowar Hamada  a Agadez
Barazanar kwararowar Hamada a Agadez Laura Angela Bagnetto

A yau shirin zai mayar da hankali kan barazanar kwararowar Hamada a sassan arewacin Najeriya, inda aka tabbatar da cewar yanzu haka jihohi 11 ne ke fuskantar wannan matsala, wadda ake bukatar daukar matakan gaggawa don kawo karshenta.

Talla

Masana a fannin inganta muhalli dai na ganin cewar matsalar ta kwararowar Hamada kusan dan adam ne ke haddasa ta da kansa, sakamakon wasu abubuwa da yake aikatawa da suka sabawa tsarin kare muhalli.

A Najeriyar dai, jihohi irin su Sokoto da Kebbi da Zamfara da Katsina da kuma Kano na cikin jihohin dake kan gaba wajen fuskantar barazanar ta kwararowar Hamada, inda masana suka ce babbar barazana ce ga muhalli da wadatar abinci da kuma lafiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.