NIMET ta gargadi manoman Najeriya kan shuka da wuri kafin saukar damina

Sauti 18:50
Wani manomi akan motar tantan yayin aiki a gonarsa dake jihar Nasarawa a Najeriya.
Wani manomi akan motar tantan yayin aiki a gonarsa dake jihar Nasarawa a Najeriya. © Alluvial Agriculture/Handout via Reuters

Shirin a wannan mako ya tattauna kan yanayin daminar bana da ake shirin shiga a tarrayyar Najeriya, a yayin da manoma suka dukufa kan shirin share gonakinsu da domin ayyukan noma, hukumar kula da hasashen yanayi a kasar NIMET, ta gargadi manoman da ka da su yi gaggawar fara shuka ,saboda ruwan saman da ya soma sauka ba wai yana nuna har daminar bana ta iso ba ne.