Yadda manoman Nijar ke shirin tunkarar daminar bana

Sauti 19:48
Wasu manoma a Jamhuriyar Nijar.
Wasu manoma a Jamhuriyar Nijar. © Chris de Bode/Panos

Da dama daga cikin kasashen yankin Sahel na fama da tarin matsalolin dake tagayara muhalli dake haddasa matsaloli masu yawa ga mutanen dake yankunan. Gurbatar muhallin na samo tushe ne daga gurgusowar hamada, da zaizayar kasa, da kekashewar wurare su koma hako, sannan a wasu yankunan ana fuskantar gusawar yashi dake binne kwarurruka da tabakuna da rijiyoyi kuma rishin sanin mahimmancin itatuwa ganin yanda ake ta kashe su ba tsari.