Muhallinka Rayuwarka

Littafin binciken a kan ayyukan 'yan bindiga a arewacin Najeriya ya fito

Sauti 22:13
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na musamman ya yi nazari ne a game da littafin da wani malami a jami'ar Dan Fodio ta Sokoto, Murtala Ahmad Rufai ya kwashe shekaru 10 yana yi a kan ayyukan 'yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya. Littafin da aka wallafa da Turanci mai taken, 'I Am a Bandit', ya fito ne da sakamakon binciken da mawallafin ya yi, tare da shawarwari da zai amfane hukumomi. Bashir Ibrahim Idris ne ya shirya ya kuma gabatar.