Rayuwata kashi na 127 (Rashin ganin jinin al’ada ga Mata)

Sauti 10:02
Mace dake fama da matsalolli da suka shafi bangaren al'ada
Mace dake fama da matsalolli da suka shafi bangaren al'ada © iStock/dragana991

Daya daga cikin matakan da mata ke kaiwa a rayuwar su, bayan kammala haihuwa, shine yanayin daina ganin jinin al’ada da suka saba yi kowanne wata, wanda ke basu damar daukar ciki. Bisa al’ada kowacce mace kan fara ganin jinin wata-wata daga shekara 9 zuwa 15 wani lokaci ma har wasu kan kai shekaru 17, kuma wannan kan tsaya ne bayan da suka kai tsakanin shekaru 45 zuwa 50.

Talla

Daukewar jinin al’adar kan rufe kofar haihuwa ga ‘ya mace kamar yadda aka saba gani.

Wata mata dauke da jinjirin ta
Wata mata dauke da jinjirin ta Getty Images / Mayte Torres

A kan wannan batu Shirin Rayuwata na wannan lokaci zai mayar da hankali. tareda Zeinab Ibrahim.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.