Rayuwata kashi na 138 (Yadda matashiya ta samar da manhajar kwarmata Fyade)

Sauti 10:01
Fyade na matsayin babbar hanyar cin zarafi da mata ke fuskanta a wannan lokaci inda a yanzu ya sauya salo ta yadda har maza bai kyalesu ba.
Fyade na matsayin babbar hanyar cin zarafi da mata ke fuskanta a wannan lokaci inda a yanzu ya sauya salo ta yadda har maza bai kyalesu ba. William WEST AFP/File

Shirin Rayuwata na wannan rana tare da Zainab Ibrahim ya mayar da hankali kan yadda wata Matashiya a jihar Kano ta arewacin Najeriya ta samar da wata manhajar kwarmata fyade da nufin kawo karshen yawaitar boye rahoton aikata fyaden da ake samu a tsakanin al'umma.