Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Tattaunawa da masu sauraro kan ranar zawarawa ta Duniya

Sauti 16:06
Galibi zawarawa da yara marayun da aka kashe iyayensu ko kuma mazajensu a rikicin na Boko Haram yanzu haka na mawuyaciyar rayuwa ba tare da taimako daga ko'ina ba.
Galibi zawarawa da yara marayun da aka kashe iyayensu ko kuma mazajensu a rikicin na Boko Haram yanzu haka na mawuyaciyar rayuwa ba tare da taimako daga ko'ina ba. REUTERS

Shirin 'Ra'ayoyin masu Sauraro' tare da Hauwa Aliyu ya tattauna ne kan ranar 23 ga watan Yunin wacce Majalisar Dinkin Duniya ta ware wa matan da mazajensu suka mutu, da nufin nazari kan kalubalen da ke addabarsu da kuma magance musu shi, tare da kare musu hakkokin su. An kiyasta cewa matan da mazajensu suka mutu a fadin duniya sun haura miliyan dari biyu da hamsin da takwas, inda da dama daga cikin su ke cikin ukuba ta rayuwa.