Wasanni

Super Eagles na neman maki daya a karawar da zata yi Ecureuils ta kasar Benin

Sauti 10:02
Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika.
Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika. © CAFOnline.com

Daga cikin tikitin 24 ko mu ce 23 bayan da Kamaru mai masaukin baki, kasashe 13 ne aka tabbatar da sun samu na su tikiti ga zaman da ake yanzu. Daga cikin bakin da ake da su a wannan ganggami ,za mu iya zana tsibirin Comoros, Gambia, Gabon , Guinee Equatorial, Masar, Tunisia, Senegal ,Zimbabwe ,Ghana ,Burkina Faso , Mali ,Guinee Conakry.

Talla

A cikin shirin Duniyar wasanni,Abdurahamane Gambo yayi tattaki zuwa Eko Otel,wurin da aka sauke yan wasan Najeriya yan lokuta kafin sun fice zuwa Jamhuriyar Benin,inda za su kara da kungiyar Ecureuils a birnin Porto Novo ranar asabar.

Dan wasan kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Ahmed Musa.
Dan wasan kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Ahmed Musa. AP - Armando Franca

A cikin shirin zaku ji ko a ina aka kwana dangane da shirin da yan Najeriya keyi na ganin sun samu nasara a wannan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.