Koma bayan wasannin motsa jiki a Najeriya

Sauti 10:30
Wasar kwallon kafa ,hanyar baiwa matasa dama samu horon da ya dace
Wasar kwallon kafa ,hanyar baiwa matasa dama samu horon da ya dace AFP - PHILL MAGAKOE

A wani sabon kokari na farfado da wasannin matasa daga tushe, a kwanakin baya Ministan Wasannin Nigeria Sunday Dare, ya gana da shugabannin hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA, inda suka tattauna a kan hanyoyin farfado da wasannin motsa jiki na matasa a Nigeria.

Talla

Baya ga ma’aikatar wasanni a Nigeria, a baya, hukumomi irin su cibiyar bada horo kan harkokin wasanni ta kasa, ta taimaka wajen samar da hazikan masu koyar da wasanni tare da ‘yan wasa da suka sha cire wa kasar kitse a wuta a gasar wasannin Afrika da ma ta duniya baki daya. 

Gasar tseren keke na daga cikin wasannin motsa jiki da ya dace matasa su mayar da hankali
Gasar tseren keke na daga cikin wasannin motsa jiki da ya dace matasa su mayar da hankali AFP/Archives

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.