Siyasa

Tsarin Rabon Dukiyar Kasa

Sauti

Koda yake galibin kasashen duniya na tanadar wasu hanyoyin samun kudaden shiga daga haraji ko albarkatun kasa,tara wannan dukiyar da rabon ta ga bangarorin gwamnati ko sassan al'umma na cigaba da kasancewa babban kalubale ga kasashe masu tasowa kamar Nigeria. Kamar yadda bincike ya nuna dai ja-in-ja tsakanin bangarorin al'umma da kuma matakan gwamnati,kan inda yakamata a ba kaso mai tsoka,iyace babbar matsalar da hukumomin da aka dorawa nauyin kasafta dukiyar kasa ke fuskanta.Koda yake Nigeria da kasar Amurka na amfani da tsarin gwamnati na tarayya da jihohi,yadda kasashen biyu ke tarawa da kuma kasafta dukiyar kasa ya banbanta. Nigeria dai na dogara ne kan albarkatun man petur wajen samun kudaden shigar ta,yayin da kasar Amurka wadda ke amfani da tsarin Jari-Hujja ke dogara kan haraji daga kamfanoni da sauran hukumomi masu zaman kan su wajen samun kudaden shiga.Sai kuma watakila banda rigingimu kan abinda matakan gwamnati ke samu daga gwamnatin tarayya,a kasa kamar Nigeria,jahilci da talauci sun haddasa wani yanayin dake sa al'umma na wa muhimmancin bin diddigin kudaden dake zuwa matakan gwamnatin su,rikon-sakainar-kashi. Shirin Duniyar Mu A Yau na wannan makon, ya duba wannan batu na rabon arzikin kasa da kuma tada-jijiyoyin wuyan da ake kan sa. Shin yaya tsarin rabon dukiyar, ya banbanta tsakanin kasa da kasa kuma menenegudummuwar al'umma wajen tabbatar da adalci a wannan daunin.