Siyasa

Ranar Mata Ta Duniya

Sauti

Ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara,ranar ce da Majalissar Dinkin Duniya ta kebe,domin Matan duniya watau International Women Day. Wannan dai rana ce ta musamman da aka ware domin duba batutuwan da suka shafi rayuwar mata tsakanin kasa da kasa. Muhimmancin wannan dai shine duba wasu daga cikin matsalolin da mata ke fuskanta ta fannin ilimi,kiwon lafiya da sauran bangarori na rayuwar,da kuma duba wuraren da hukumomi da sauran kungiyoyi masu zaman kansu zasu taimaka.Sai dai yayin da ake bukin zagayowar wannan rana,mata musamman a kasashe masu tasowa na juyayin yadda makomar su ta kasance a gudanar siyasa da gwamnati. Karancin ilimin zamani,al'adu da wasu sharudda na addini,na cigaba da takaita gudummuwar mata a hidima da gudanar gwamnati.Koda yake Nigeria kamar sauran kasashe masu tasowa,ta sa hannu kan yarjejeniyar kasa da kasa da aka cimmawa a taron mata na duniya da aka gudanar a birni Beijing na China,samun kashi 30 cikin 100 na mukaman gwamnati da siyasa,na cigaba da kasaacewa babban kalubale,shekara sama da 10 bayan wannan taron na Majalissar Dinkin Duniya (United Nations).Shirin Duniyar Mu A Yau na wannan makon,ya duba makomar mata a kasashe masu tasowa kamar Nigeria,matsalolin dake wa matan shamaki ko tarnaki wajen cimma daidaito da kuma wasu daga hanyoyin da watakila za'a bi domin inganta rayuwar matan.