Siyasa

Alkawurran 'Yan Takara

Sauti

Kasa da makonni 2 ya zuwa zabubbukan kasa a Nigeria,'yan takarar mukaman siyasa na cigaba da zariyar tallata kansu a kampe da gangamin siyasa. Wadannan gangamin da tarurruka dai kan kasance wani dandali na daukar alkawurra ka masu kada kuria,domin samun goyon bayan su wajen zaben 'yan takara.Sai dai kuma bayan shekaru suna kada kuria,ba tare ganin an chika masu wadannan alkawurran ba,yanzu jama'a sun fara tunanin cewa anya kuwa ba yaudarar su 'yan siyasa keyi ba? Kamar yadda bincike ya nuna dai,jahilci da wani zibin takauci,sun kasance dalilan da suka sa yawanci jama'a na sanyi-gwiwar tunkarar wakilan su,kan wadannan alkawurran da suka yi yayin neman kuria.Shirin Duniyar Mu A Yau na wannan makon,ya duba wadannan alkawurran da 'yan takara keyi kafi zabe,tasirin rashin chika su a mulkin dimokiradiyya da kuma yadda watakila yadda al'umma zata dauki nauyin bin diddigin wadannan alkawurran,domin tabbatar da cewa an chika su bayan hawa kan karagar mulki.