Siyasa

Rahoto Kan Bangar Siyasa A Najeriya

Sauti

A Najeria dai daga cikin matsalolin dake kafar Ungulu ga wanzuwar ingantacciyar Dimokradiyya shine sha'anin bangar siyasa, wannan kuwa na aukuwane bisa yadda 'yan siyasa a kasar ke amfani matasa domin yin barazana ga abokan hamayyarsu. Yanzu haka ana cigaba da samun matasa dake kutsa kansu cikin wannan halayyar, duk da cewar wasu na yiwa bangar kallon babbar matsa ga al'umma.Dangane da hakanne wakilin mu na sakkwato Faruk Muhammad Yabo, ya hada mana wannan rahoton.